ha_tn/hos/10/10.md

859 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana.

zunubi ribi biyu

Wannan yana nuni da yawan zunuban Isra'ila.

Ifraimu horarriyar karsana ce mai jin dadin yin sussuka

Karsana tana jin dadin sussuka domin sukan yi ta yawo a sake ba tare da nauyin kaya ba. Yahweh yana nufin cewa ya bar jama'ar Isra'ila su sake su ji dadin rayuwa.

Na sa wa kyakkyawan wuyarta karkiya.

A nan, "karkiya" tana nufin shan wahala ko bauta. Yahweh ya yi jama'ar Isra'ila alheri, amma mutanen sun ci amanarsa. Saboda haka, zai hukunta su, ya korre su su zama bayi.

Yahuza za ta ja garmar noma; Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya

A nan, "Yahuza" tana nufin jama'ar masarautar kudu, "Yakubu" kuma tana nufin masarautar arewa. Wannan yana nufin Allah zai kawo lokutan wahala wa duka masarautu biyun.

garmar bajiya

abin da ake mora wajen baje kasa, a rufe iri bayan an yi noma.