ha_tn/hos/10/09.md

970 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana.

kwanakin Gibeya

Watakila wannan yana nuni da miyagun ayyukan kabilar Bilyaminu da aka lissafta a Mahukunta 19-21. Duba yadda ka fassara wannan a 9:8.

kuka yi ta ci gaba

Wannan nassin yana nufin cewa mutanen yanzu sun ci gaba da aikata irin ayyukan da kakanninsu suka yi a Gibeya. A.T: "kuma kuna tunani kamar yadda suka yi".

Ashe, yai ba zai tarshe 'ya'yan zunubi a Gibeya ba?

Yahweh ya mori tambaya domin jaddada cewa wadanda suke a Gibeya, wadanda suka aikata zunubi, tabbas za su yi fama da yaki. Kuma wannan yana maganar yadda mutanen za su yi fama da yaki sa'adda abokan gabansu suka zo kamar yakin mutum ne wanda zai kama su. A.T: "Tabbas, yaki zai abka wa wadanda suka aikata zunubi a Gibeya" ko "Hakika, abokan gaba za su kai hari kan wadanda suka aikata zunubi a Gibeya".

'ya'yan zunubi

A nan, "'ya'ya" karin magana ce mai nufin "masu irin halin abu". A.T: "wadanda suke aikata zunubi" ko "masu mugunta".