ha_tn/hos/10/07.md

836 B

Sarakunan Samariya za su bace

Za a iya fadin wannan kai tsaye. A.T: "Assuriyawa za su hallaka sarkin Samariya".

kamar dan guntulen katako a bisa ruwa

Wannan yana nufin sarkin Samariya zai rasa taimako kamar dan guntulen katakon da igiyoyin ruwa ke karkadawa gaba da baya.

Za a hallaka masujadan tuddai... inda suke yin zunubi

Za a iya fadin wannan kai tsaye: A.T: "Assuriyawa za su hallaka masujadan tuddai na Isra'ila, inda mutanen suke aikata mugunta".

Za su ce wa manyan duwatsu, "Ku rufe mu!". Su ce wa tuddai, "Ku fado bisa kanmu!"

Mutane ba su saba yin magana da abubuwan ba su tunani ko jinsu ba. Mai fassara yana iya samu wata hanya dabam bayyana wannan nassin, idan yarensu bai ba da damar irin wannan furcin ba. A.T: "Mutanen za su ce, 'Da ma duwatsu su rufe mu!' kuma 'Muna fatar tuddai za su fado a kanmu!'".