694 B
694 B
Muhimmin Bayani:
Yusha'u yana magana game da Isra'ila.
amma me sarki zai yi mana
Mutanen za su ce sarkinsu ba zai iya taimakonsu ba. A.T: "Ko da muna da sarki, ba zai iya taimakonmu ba".
Surutai kawai suke yi
A nan, "surutai" tana nufin karairayi. A.T: "Suna fadin karairayi".
Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona
Abin da mutanen suke kira hukunci a dokarsu da shari'arsu, ana maganarsa kamar shuka ce mai tsirowa. A.T: "Saboda haka shari'arsu ba ta adalci ba ce; sai dai, tana da illa".
kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona
Karairayinsu da rashin adalcinsu suna yaduwa ko'ina a kasarsu, suna cutar da kowa kamar shuka mai dafi.