ha_tn/hos/10/01.md

672 B

Muhimmin bayani:

Yusha'u yana magana game da Isra'ila.

Isra'ila kuringar inabi ce mai bansha'awa, wadda take ba da 'ya'ya

Ana maganar Isra'ila kamar kuringar inabi mai bayar da 'ya'ya sosai. Akwai dan lokacin da mutanen suka arzuta, suka yi karfi.

kuringar inabi mai bansha'awa

Kunringar da ke ba da 'ya'ya fiye da yadda aka saba samu.

Kara yawan arziki... kara yawan kasa

Dukka wadannan biyu suna nufin yadda wadatar mutanen take karuwa, suna kara karfi da arziki.

Zuciyarsu ta munafunci ce

"Zuciya" tana nufin yanayinsu a ciki. "Suna da yaudara".

Yanzu tilasa za su dauki hakkin laifinsu

"Yanzu ne lokacin da Yahweh zai hore su saboda zunubansu".