776 B
776 B
Muhimmin Bayani:
Yusha'u, annabi, yana magana.
Na ga Ifraimu, kamar Taya, an shuka ta a kasa mai danshi
"Shuka" tana nufin kasancewa a wurin mai tsaro. A.T: "A da kasar Isra'ila tana da kyau kamar birnin Taya, kamar bishiyar da wani ya shuka a kasa mai danshi".
amma Ifraimu tana fitar da 'ya'yanta
"'Ya'ya" su ne jama'ar wannan kasar. A.T: "amma jama'ar Isra'ila za su fitar da 'ya'yansu".
Ka ba su, Yahweh - me za ka ba su? Ka ba su
Yusha'u ya yi amfani da tambaya wajen jaddada cewa Yahweh yana so ya ba mutanensa abin da ya cancance su. A.T: "Wannan ne abin da na roke ka, Yahweh, ka ba su: ka ba su".
cikin da ba ya haihuwa
"Ba ya haihuwa" yana nufin cikin da ake baraswa, jaririn ya mutu. Yusha'u yana roko domin dukkan matayen Isra'ila su zama haka.