ha_tn/hos/09/10.md

536 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana.

Sa'adda na iske Isra'ila

Wannan yana nufin sa'adda Yahweh ya fara dangantakarsa da farko da jama'ar Isra'ila ta wurin kiransu mutanensa na musamman.

kamar inabi. Na ga kamanninku kamar nunar fari na 'ya'yan baure

Wadannan maganganu guda biyu suna jaddada yanayin da suke faranta ran mutum. Wannan yana nufin Yahweh ya ji dadi sosai sa'adda dangantakarsa da jama'ar Isra'ila ta fara.

Ba'al Feyor

Wannan sunan wani tudu ne a kasar Mowab inda ake yi wa allahn karyan nan, Ba'al, sujada.