ha_tn/hos/09/08.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Yusha'u, annabi, yana magana.

Annabin mai tsaro na Allahna ne a bisa Ifraimu

"Mai tsaro" yana tsaron wajen birninsa don ya ga ko hatsari yana zuwa. Kashedin da annabin yake yi wa mutanen sa'adda suke zunubi, kuma suna cikin hatsarin fuskantar hukuncin Allahnsa, ana magarsa a nan kamar shi ne mai tsaron birnin. A.T: "Annabin kamar mai tsaro ne na Allah bisa Ifraimu".

Annabin mai tsaro na Allahan ne bisa Ifraimu

Wadansu juyin sun fassara wannan nassin kamar "Annabin, tare da Allahna, shi ne mai tsaron Ifraimu".

Annabin shi ne

Wannan yana nufin annabwa gaba daya da Allah ya zaba. A.T: "Annabawan su ne" ko "Annabawan gaske su ne".

Ifraimu

A nan, "Ifraimu", yana wakilcin dukkan jama'ar Isra'ila.

akwai tarkon kama tsuntsu a dukkan hanyoyinsa

"Tarkon kama tsuntsu" ana amfani da shi wajen kama tsuntsu. Wannan yana nufin cewa mutanen Isra'ila suna yin duk abin da za su yi don dakatar da annabawan Allah: A.T: "mutanen suna dana masa tarko duk inda ya tafi" ko "mutanen suna yin duk abin da za su iya yi don su cutar da shi".

Zun yi zurfi cikin kazanta kamar a kwanakin Gibeya

"Jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, sun kazantu kamar yadda suka yi a Gibeya da dadewa". Mai yiwuwa wannan magana ce mai nuni da ayyukan bankyama na kabilar Bilyaminu da aka lissafta a Mahukunta 19-21.