ha_tn/hos/09/07.md

983 B

Muhimmin Bayani:

Yusha'u, annabi, yana magana.

Ranar hukunci tana zuwa; ranakun ramako suna isowa

Yusha'u ya yi wadannan maganganu biyu iri daya domin jaddada cewa Yahweh zai hukunta jama'ar Isra'ila domin miyagun ayyukansu, nan ba da jimawa ba.

Annabin wawa ne, mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne

Wadannan kalamai suna nufin abu daya ne. Ma'anar tana iya zama 1) mutanen sun dauki annabawan a matsayin mahaukata, ko 2) annabawan sun haukace saboda zunuban da mutanen suka aikata.

Annabin wawa ne, mutumin da yake da ruhu kuma mahaukaci ne

A nan, "annabi" da "mutum mai ruhu" duk suna nufin mutumin da yake cewa yana karbar sakonni daga wurin Allah. Yana nufin cewa wadannan mutanen annabawan karya ne, kuma suna tunani ne kawai cewa suna karbar sakonni daga wurin Allah.

saboda yawan muguntarku da kiyayyarku

Kalmomin "yawan mugunta" da "yawan kiyayya" suna da ma'ana masu kama. Muguntar mutanen ta bayyana kanta cikin kiyayyarsu ga Yahweh da annabawansa.