ha_tn/hos/09/05.md

1.4 KiB

Muhimmin Bayani:

Yusha'u, annabi, yana magana.

Me za ku yi a kayyadaddiyar ranar idi, ranar idin Yahweh?

Yusha'u yana amfani da wannan tambayar domin jaddada cewa mutanen ba za su ci gaba da yin idodinsu sa'adda abokan gabansu suka yi maishe su bayi ba. A.T: "Ba za ku iya bukin idin da Yahweh ya kayyade muku ba".

kayyadaddiyar tanar idi... ranar idin Yahweh

Duka wadannan biyu suna nufin abu daya.

idan sun tsira

A nan, "su" yana nufin mutanen Isra'ila ne. Za ka iya ci gaba da wannan maganar kamar wani ne yake magana da su. A.T: "idan kun tsira".

Masar za ta tattara su, Memfis za ta binne su

Masar da Memfis suna nufin mutanen da suke zaune a can. A.T: "mayakan Masar za su kama ku. Za ku mutu a can, kuma mutanen Memfis za su binne ku" (UDB)

Abubuwan tamaninsu na azurfa kuwa - kayuyuwa za su mallake su

Ana maganar kayuyuwan da ke girma a wuraren da Isra'ilawa suka adana azurfarsu kamar kayuyuwan mutane ne, abokan gaba, wadanda za su kwace abubuwan tamani na Isra'ilawa don kansu. A.T: "Kayuyuwa masu tsini za su yi girma a wuraren da suke adana dukiyarsu ta azurfa".

kayuyuwa masu tsini za su mallake su, sarkakkiya za ta tsiro a alfarwarsu

A nan, "kayuyuwa masu tsini" da "sarkakkiya" suna nufin abu daya. Girmar kayuyuwa da sarkakkiya tana wakiltan kasar da ta zama kango, kamar hamada.

alfarwarsu

A nan, "alfarwa", tana wakiltan gidajen Isra'ilwa.