923 B
923 B
Muhimmin Bayani:
Yusha'u, annabi, yana magana.
Kasar Yahweh
Wannan furcin yana nuna alamar cewa Yahweh ya ci gaba da ganin kasar Isra'ila a matsayin mallakarsa, ba mallakar Isra'ilawa ba.
haramtaccen abinci
Wannan abinci ne da ya kamata Isra'ilawa su ki ci domin zai kazantar da su a gaban Yahweh.
Abinicinsu zai zama irin na masu makoki
A nan, "abincin masu makoki" yana nufin abin da mutane suke ci sa'adda suke makoki, domin sun kazantu, kuma ba arbabbu ba ne a gaban Allah. Wannan yana nufin Yahweh zai dauki hadayun mutanensa su zama kazantattu, kuma ba zai karbe su ba.
Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai; ba za su kai shi haikalin Yahweh ba
Mutanen Isra'ila za su sami abincin ci, amma Yahweh ba zai karbi abincin a matsayin sadaka ba.
ba za su kai haikalin Yahweh ba
Ana maganar kazantaccen abincin kamar yana iya zuwa wurare da kansa. Hakika, mutane ne suke kai shi da kansu.