ha_tn/hos/09/01.md

727 B

Muhimmin Bayani:

Yusha'u, annabi, yana magana.

Masussuka da wurin matsa ruwan inabi ba za su ciyar da su ba

Wannan yana bayyana masussukar da wurin matsa ruwan inabi kamar su mutane ne da za su iya ciyar da wani. Wannan yana nufin cewa girbin ba zai zama da albarka ba sosai har hatsin da ke masussuka ya biya bukatar mutane, kuma ba zai samar da isasshen inabi domin a matsa isasshen ruwan inabi ba.

masussuka

Wadannan wurare ne masu fadi, inda ba sussuka kadai ake yi ba, amma ana yin bukukuwan al'umma da na addini. Karuwai na haikali sukan zo domin su taimaki mazaje wajen bukin girbi da bukukuwan gumaka.

Sabon ruwan inabi kuma ba zai ishe su ba

Ba za a sami isasshen inabin da zai samar da ruwan inabi ba.