ha_tn/hos/08/08.md

753 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana.

Isra'ila tana cikin al'ummai

"Ciki" tana nufin an yi nasara a kansu, an kwashe su bauta. Za a iya fadin wannan kai tsaye. A.T: "Abokan gaban Isra'ila sun kwashi Isra'ilawa zuwa wata kasa".

kamar jakin jeji

Mutane sun san jakuna da taurinkai. Wannan yana nufin jama'ar Isra'ila sun ki su saurari Yahweh, amma sai suka tafi wurin mutanen Assuriya neman taimako.

Ifraimu ta sama wa kanta samari/abokai

Ana maganar kawancen Ifraimu da sauran kasashe kamar sun biya don su zama karuwai na Ifraimu. A.T: "Mutanen Ifraimu suna biyan wadansu kasashe domin su kare su" (UDB)

ta wurin tunanin nawayar sarkin sarakuna

Wato, saboda sarkin Assuriya, wanda kuma akan kira "Babban Sarki", zai azabtar da jama'a.