ha_tn/hos/07/08.md

713 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana.

Ifraimu ta hada kanta da al'ummai

Mai yiwuwa wannan nuni ne ga yunkurin da sarkin masarautar arewa ya yi na hada kawance da sauran al'ummai domin neman kariya daga hari.

Ifraimu kamar wainar da ba a juya ba ce

Za a iya fadin wannan kai tsaye. A nan, "Ifraimu" tana nufin masarautar arewa ta Isra'ila. Kasar ba ta da karfi, kamar wainar da ba a juya a tanderu domin ta yi karfi ba. A.T: "Mutanen Ifraimu suna kama da wainar da babu wanda ya juya".

Furfura ta faso musu

A nan, "furfura", tana wakilcin tsufa.

amma ba su sani ba

Amma, wannan "tsufa" hanya ce ta fadin cewa masarautar arewa ta rasa karfi a kai a kai, domin kasar ba ta sani cewa ta "tsufa" ba.