732 B
732 B
Muhimmin Bayani:
Ana bayyana makarkashiyar jami'an fadar sarki. Fushinsu ne ya ingiza su don su kashe sarkinsu.
Zukatansu kamar tanderu
Wannan yana nufin kamar yadda wuta take kuna a tanderu, mutanen nan suna da zafin kishin mugunta a cikinsu.
Fushinsu na ci dare farai
Kalmar "ci dare farai" tana nufin abin da ke kuna ba tare da harshen wuta ba. A.T: "fushinsu yana ta girma a hankali, a boye".
yana ci bal-bal kamar harshen wuta
Ana maganar zafin fushinsu kamar wuta mai zafin gaske ne. A.T: "yakan zafafa kwarai".
Dukkansu suna da zafi kamar tanderu
Wannan yana kwatanta fushinsu da zafin da ke zuwa daga tanderu.
suna kashe masu mulkinsu
Kamar wannan yana nufin jami'an fadar sarki suna kashe sarakansu.