ha_tn/hos/07/03.md

1.1 KiB

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana. Nassin Ibraniyancin ba a bayyane yake sosai a wadansu wurare ba. Amma, mutane da yawa suna fassara shi a matsayin yana bayyana jami'an masarauta a amatsayin maciya amanar Allah, kuma suna shirin kashe sarki, sa'annan su aiwatar da shirye-shiryensu. Kamar wannan al'amarin ya faru fiye da sau daya. An ambaci wadannan laifuffukan kamar kwatanci ne na muguntar da kasar ta dulmuya kanta a cikin.

Dukkansu mazinata ne

Mutanen sun aikata zina ta ruhaniya ta wurin bautar gumaka da cin amanar Yahweh. Mai yiwuwa ma suna cin amanar mazajensu ko maayensu ta wurin kwana da wadansu mutane.

kamar tanda da aka zafafa

Za a iya furta wannan kai tsaye. Wannan yana nufin mutanen suna da zafin sha'awar aikata mugunta. A.T: "kamar tandan da mai yin gurasa ya zafafa".

cude kullu

Wannan wani mataki ne na yin gurasa.

A ranar bukin sarkinmu

Mai yiwuwa wannan buki ne da sarki yake yi.

Yakan yi cudanya

Watakila wannan yana nufin hadewa ko cudanya da wani. Yana iya nufin cewa sarkin yana hada kai da jami'ansa wajen yin ba'a kan abubuwa ko mutanen da bai kamat a ayi wa ba'a ba, har Allah kansa.