ha_tn/hos/07/01.md

655 B

Muhimmin bayani:

Yahweh yana magana.

Ina so in warkar da Isra'ila

Sa Isra'ila ta yi biyayya da Allah kuma, su zama masu samun albarkunsa, an yi maganr kamar warkarwa ce.

gama suna yaudara

Wadannan mutanen suna saye da sayarwa da rashin gaskiya.

'yan fashi

Wannan kungiya ce ta mutane masu kai wa wadansu mutane hari babu dalili.

ayyukansu sun kewaye su

Mai yiwuwa ana maganar miyagun ayyukan mutanen a nan kamar wadansu mutane ne da suke shirye don su tuhume su da laifuffukansu.

ina ganinsu

"Ina ganinsu" yana nufin kasancewar Allah, ko kuma sanin Allah. "Shaidun", wato, miyagun ayyukan, suna a gaban Allah domin su kawo kararsu.