ha_tn/hos/06/04.md

781 B

Furcin Sadarwa:

Yahweh yana magana.

me zan yi da ke?

Allah yana nuna cewa hakurinsa ta kawo karshe, kuma abin da ya rage kawai shi ne hukunci. A.T: "yana da wuya sanin abin da za a yi da ku!"

Na sassare su ta wurin annabawansu

Ta wurin annabawansa, Yahweh ya yi shelar hallakarwa a kan kasar nan mai tawaye. Hallakarwar, wanda a nan aka kira "sassarewa", tabbasa ne kamar hukuncin.

Hukuntanka suna kama da hasken da ke ketowa

A nan, Yusha'u yana magana da Allah. Mai yiwuwa yana nufin cewa sa'adda Allah ya yi shelar doka don wani ya mutu a matsayin hukunci, yana kama da ketowar walkiya mai bugu (duba UDB). Ko kuma, watakila yana nufin cewa dokokin Allah suna ba mutane damar sanin gaskiya, kamar yadda haske yakan haskaka abubuwa.

Hukuntanka

"Dokokin Yahweh"