ha_tn/hos/05/12.md

864 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Yahuza da Isra'ila.

Zan zama kamar asu ga Ifraimu, kamar ruba ga mutanen Yahuza

Asu a kan ulu da ruba a kan katako, duk suna da ta'adi. Yahweh zai hallaka duk kasashen biyu.

asu... ruba

Wadannan kalmomi biyu, an fassara su a hanyoyi da yawa, domin ma'anar kalmar Ibraniyancin yana iya zama da fadi sosai ko kuma ma ba a tabbatar da ita ba.

Sa'adda Ifraimu ta ga ciwonta, Yahuza kuma ta ga rauninta

Da Ifraimu (masarautar arewa ta Isra'ila) da Yahuza (masarautar kudu ta Isra'ila) sun gane cewa suna cikin hatsari.

sai Ifraimu ta je wurin Assuriya, Yahuza kuwa ta aika 'yan sako wurin babban sarki

Ifraimu da Yahuza sun roki taimako daga Assuriya, maimakon neman taimakon Yahweh. "Babban sarki" wani take ne na sarkin Assuriya.

Amma ba zai iya ba

A nan, "ba zai iya ba" yana nufin sarkin Assuriya.