ha_tn/hos/05/10.md

924 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Yahuza da Isra'ila.

Shugabannin Yahuza sun zama kamar masu kawar da dutsen kan iyaka

"Kawar da dutsen kan iyaka" yana nufin kawar da alamar da ta bambanta kan iyakar kasa, wanda laifi ne bisa ga dokar Isra'ila.

Zan zubo musu da fushina kamar ruwa

Fushin Yahweh a kan Yahuza zai zama kamar babbar magudanar ruwar da za ta hallaka su. A cikin nassi, akan yi maganar jin-zuci da halin da'a kamar suna da yanayin ruwa.

Ana danne Ifraimu; shari'a ta murkushe ta

Za a iya fadin wannan kai tsaye. An yi wannan furcin sau biyu don a jaddada batun. A nan "Ifraimu" yana nufin mutanen masarautar arewaci ta Isra'ila. A.T: "Zan yi wa mutanen Isra'ila horo mai tsanani".

ta bi gumaka

A nan, "bi" yana nuni da sujada.

gumaka

Kalmar Ibraniyanci da aka fassara a nan a matsayin "gumaka", ba a tabbatar da ma'anarta ba, kuma sabobbin juyi sun fassara ta a hanyoyi da yawa.