ha_tn/hos/05/05.md

1.2 KiB

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Isra'ila.

Girman kan Isra'ila yana ba da shaida a kanta

Wannan yana bayyana "girman kai" a matsayin mutum wanda yake ba da shaida a kan mutanen Isra'ila a kotu. Halayyarsu ta girman kai ta nuna cewa suna da laifin daina yi wa Yahweh biyayya.

saboda haka Isra'ila da Ifraimu za su yi tuntubi cikin laifinsu; Yahuza ma za ta yi tuntube tare da su

Masarutun nan biyu za su yi wa Allah rashin biyayya gaba daya saboda girman kansu da zunubinsu.

Sun ci amanar Yahweh, sun haifi shegu

Ma'anar tana iya zama 1) wannan yana nufin cewa Isra'ilawa suna aure daga wadansu al'ummai, suna haifan yara tare da su, ko 2) wannan yana nufin iyayen Isra'ilawa sun ci amanr yahweh, kuma suna koya wa 'ya'yansu bautar gumaka.

Yanzu bukukuwan amaryar wata za su cinye su da gonakinsu

Ya kamata mutanen Isra'ila su yi buki a lokacin sabuwar wata. A nan, kamar wannan maganar bayyana amaryara wata a matsayin muguwar dabbara da za ta cinye jama'a da gonakinsu. Amma, yana da wuya a fassara wannan maganar; juyi da yawa sun fassara ta ba a bayyane sosai ba. Amma, ma'anar dai gaba daya ita ce, hakika Allah zai hori jama'ar Isra'ila domin rashin amincin da suka yi masa.