ha_tn/hos/05/03.md

896 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Isra'ila.

Na san Ifraimu, Isra'ila kuma ba a boye take a gare ni ba

A nan, "Ifraimu" da "Isra'ila" duk suna nufin mutanen da suke zaune a masarautar arewa ta Isra'ila. A nan, Allah yana cewa ya san yadda suke da kuma abin da suke yi.

Ifraimu, yanzu kin zama kamar karuwa

Ana gabatar da Ifraimu a matsayin karuwa, domin mutanen sun yi wa Allah rashin aminci, kamar yadda karuwa ba ta da aminci ga kowane mutum.

gama halin karuwanci yana cikinsu

Wannan yana nufin suna da sha'awar yi wa Allah rashin aminci. Suna marmarin bautar gumaka.

su komo wurin Allah... ba su san Yahweh ba

Mai fassara zai iya bayyana wannan a matsayin "su komo wurina... ba san ni ba", ko "su juyo wurina... ba su san ni ba, Yahweh".

kuma ba su san Yahweh ba

Isra'ila ta daina yi wa Yahweh biyayya a kowace hanya. Ba su dauki Yahweh a matsayin Allahnsu ba.