ha_tn/hos/05/01.md

939 B

Furcin Sadarwa:

Yahweh yana magana game da Isra'ila.

Kun zama tarko a Mizfa, da ragar da aka shimfida a Tabor

Tarko da raga, duk ana amfani da su wajen kama dabba. A wannan yanayin, firistoci da gidan sarauta sun kirkiro dabarun nisanta jama'a daga Yahweh, yayinda suke yaudararsu zuwa ga bautar gumaka. Mizfa da Tbor wurare ne na bautar gumaka a kasar Isra'ila.

Masu tawaye sun yi zurfi cikin kisa

A nan "masu tawaye" yana nufin dukkan mutanen da suka juya wa Yahweh baya, sa'annan "zurfi cikin kisa" yana nufin zub da jinin mutane marasa laifi, ko yanka dabbobin da akan yi hadaya da su a bautar gumaka.

Masu tawaye

Mai fassara yana iya bayyana wannan a matsayin, "Ku masu tawaye", domin Allah yana magana ne da jama'a masu tawaye na Isra'ila.

cikin kisa

Wadanus juyi na zamani sun fassara kalmar Ibraniyancin a matsayin mugunta.

Zan hore su duka

Mai fassara yana iya bayyana wannan a matsayin "Zan hore ku duka".