ha_tn/hos/04/17.md

668 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Isra'ila.

Ifraimu ya hada kansa da Gumaka; a rabu da shi

A nan, "Ifraimu" yana nufin jama'ar masarautar arewacin Isra'ila. Sun zabi su bauta wa gumaka, maimakon Yahweh. Yahweh yana umurtar Yusha'u kada ya yi kokarin tsautar musu. Jama'ar Isra'ila ba za su saurara ba.

sarakaunanta suna kaunar kunyarsu

Shugabannin ba su jin kunyar abin da suke aikatawa sa'adda suke bautar gumaka suna juya wa Yahweh baya.

Iska za ta kunshe ta cikin fukafukinta

A nan, "iska" tana nufin hukuncin Allah da fushinsa a kan kasar Isra'ila. Yahweh zai kyale mayakan abokan gaba su yi nasara kan jama'ar Isra'ila, su dauke su bayi.