ha_tn/hos/04/15.md

1.2 KiB

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Yahuza da Isra'ila.

kada mutanen Yahuza su yi laifi

Allah ya san yadda Isra'ila ta cika da zunubi, kuma ba ya so Yahuza ta aikata irin wannan sha'anin.

Kada ku tafi Gilgal, ko ku haura Bet-awen

An yi wa mutanen Yahuza kashedi cewa, kada su tafi biranen Gilgal ko Bet-awen don bautar gumaka a wadannan wuraren. A da, Gilgal wuri ne inda ake yi wa Yahweh sujada, amma ya zama wurin bautar gumaka.

Bet-awen

Wannan birni ne a kan iyaka tsakanin masarautar arewa ta Isra'ila da kabilar Bilyaminu a masaautar kudu.

kamar alfadari mai taurin kai

An kwatanta Isra'ila da dan alfadari da ba ya yi wa ubangidansa biyayya.

Yaya Yahweh zai yi kiwonsu a kamar tumaki a makiyaya mai fadi?

Yahweh yana amfani da tambaya wajen jaddada cewa ba zai ci gaba da kula da |isra'ila ba, domin suna da taurin kai. An yi maganar yadda Yahweh ya daina kula da mutanensa kamar shi makiyayi ne wanda ba zai kula da tumakinsa a makiyaya ba, domin suna da taurin kai. A.T: "Yahweh ba zai zama makiyayin mutane masu tawaye ba" ko "Saboda haka, Yahweh ba zai ci gaba da kulawa da su ba".

Yaya Yahweh

A nan, Yahweh yana magana game da kansa kamar wani ne dabam. Za a iya fadin maganar kamar shi yake yin ta. A.T: "Yaya ni zan".