ha_tn/hos/04/13.md

533 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana game da Isra'ila.

a bisa kwankolin duwatsu... a bisa tuddai

Mutanen su saba kafa gumaka a wadannan wuraren, wanda akan kira "manyan wurare" a Tsohon Alkawari.

karuwai na haikali

Wadannan mata ne masu aikata jima'i da mzana da suka zo bautar wadansu gumaka. An dauki wannan a matsayin wata ibada ce ta bangirma ga allolin karyan nan.

Saboda haka, wannan jama'ar, mara fahimta, za ta fadi

Yahweh zai hallaka kasar Isra'ila domin ba su fahimci umurnan Allah ko su yi biyayya da su ba.