ha_tn/hos/04/06.md

913 B

Muhimmin Bayani:

A 4:6 Yahweh yana magana da fristoci game da jama'ar Isra'ila. Amma a 4:7, yana magana game da firistocin, ba su ba. mai yiwuwa ne ga mai fassara ya bi misalin UDB, wanda ke nuna Yahweh yana magana da firistoci kuma a 4:7.

Mutanena sun lalace sabodarashin sani

za a iya fadin wannan kai tsaye. A.T: "Jama'ata suna hallaka domin ku, firistoci, ba ku koyar da su sosai game da ni, yadda za su yi mini biyayya ba".

sani

A nan, "sani" yana nufin sanin Allah.

Sun sauya darajarsu da kunya

Ma'anar tana iya zama 1) "daraja" kamance ne da ke wakiltar Yahweh, sa'annan "kunya" kamance ne mai wakilcin gumaka. A.T: "Sun daina yi mini sujada, Ni Allahnsu mai girma, yanzu suna bautar gumaka" ko 2) wadansu juyin Littafi Mai Tsarki sun fassara wannan zuwa "zan sake darajarsu da kunya". Wannan yana nufin Yahweh zai dauke abubuwan da firistoci suke darajantawa, ya sa firistocin su ji kunya.