ha_tn/hos/03/01.md

666 B

Ka koma kuma, ka kaunaci mace, wadda mijinta yake kauna, amma kuma mazinaciya ce

Wannan yana nuni da 1:1. Yahweh yana sake fada wa Yusha'u kuma cewa ya kaunaci mazinaciyar mace.

Ka kaunace ta kamar yadda Ni, Yahweh, nake kaunar jama'ar Isra'ila

Ta wurin kaunar mazinaciyar macen nan, Yusha'u zai zama misalin kaunar Yahweh domin Isra'ila.

suna bin wadansu gumaka, suna kaunar wainar zabibi

Mutane suna cin wainar zabibi ko ta baure a lokutan bukukuwa, inda suke bautar allolin karya.

tsabar azurfa goma sha biyar da buhu biyu na sha'ir

Wannan shi ne farashin sayen bawa.

tsaba goma sha biyar

"tsaba 15"

buhu biyu na sha'ir

"buhun sha'ir biyu"