ha_tn/hos/02/23.md

810 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana da Yusha'u game da abin da zai yi domin Isra'ila.

Zan dasa ta a kasa domin kaina

Sa'adda Allah ya kiyaye jama'arsa lafiya, ya arzuta su a kasarsu kuma, ana maganrsu kamar amfanin gona. AT: "Zan kula da jama'ar Isra'ila kamar yadda manomi yake shuka kayayyakin gona ya kula da su" (UDB).

Lo Ruhama

Wannan sunan yana nufin "ba jinkai". Mai fassara yana iya zaben ya nuna wannan ma'anar a matsayin sunan. Duba yadda ka fassara wannan a 1:6. AT: "Ba Jinkai"

Lo Ammi

Wannan sunan yana nufin "ba mutanena ba". Mai fassara zai iya morar wannan ma'anar a matsayin sunan. Duba yadda ka fassara wannan a 1:8. AT: "Ba Mutanena Ba"

Ammi Attah

Wannan sunan yana nufin "ku mutanena ne". Mai fassara yana iya morar wannan ma'anar a matsayin sunan. AT: "Ku Mutanena ne".