ha_tn/hos/02/18.md

569 B

Furcin Sadarwa:

Yahweh yana magana da Yusha'u game da abin da zai yi wa Isra'ila.

A wancan rana

Ana morar wannan furcin don magana game da lokaci mai zuwa na maido da dangantaka tsaknin Isra'ila da Yahweh.

zan yi alkawari dominsu

Sabon alkawarin Yahweh zai hada da zaman lafiya na dabbobi.

Zan kakkarya baka da takobi, in sa yaki ya kare a kasar, sa'annan za su yi zamansu lami lafiya

Yahweh zai nisanta magabtan Isra'ila daga gare su, ba za a sake yaki ba, jama'ar za su yi zaman lafiya.

zamansu lami lafiya

Wannan furcin yana nuni da zaman lafiya.