ha_tn/hos/02/16.md

548 B

A wancan ranar

Wannan yana nuni da ranar da Isra'ila ta zabi ta bauta wa Yahweh Shi kadai.

furcin Yahweh

"abin da Yahweh ya shaida" ko "abin da Yahweh ya rantse". Duba yadda ka fassara wannan a 2:12.

Mijina

Wannan yana nufin jama'ar Isra'ila za su kaunaci Yahweh, su yi masa aminci, kamar yadda mace take yi wa mijinta.

Ba'al

"Ba'al" yana nufin "ubangida", kuma yana nuni da allahn karya da Kan'aniyawa suke bauta wa.

Gama zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta

Isra'ilawa ba za su sake ambaton sunayen Ba'al da gumaka ba kuma.