ha_tn/hos/02/02.md

1.4 KiB

Muhimmin Bayani:

Yahweh yana magana da Yusha'u.

kara

Wannan korafi ne da wani ya kai game da wani a kotun shari'a.

uwarka

A nan, "uwa" na nufin kasar Isra'ila.

domin ita ba matata ba ce

Yahweh yana fadin cewa, Isra'ila, wacce a nan aka yi magana a kanta a matsayin mace, ta daina hidimarta ta macen aure ga Allah. Maimakon haka, sai Isra'ila ta juya daga binsa da kuma yi masa sujada.

kuma ni ma ba mijinta ba ne

Yahweh ba zai iya ci gaba da dangantaka da kasar Isra'ila kamar yadda miji zai yi da matarsa ba.

kuma ayyukanta na zina

Macen aure da take mazinaciya, tana barin mijinta, ta kwana da wani maniji. Haka Isra'ila ta rika yi wa Yahweh.

daga tsakanin nononta

Wannan misalin yana nuna cewa Isra'ila ta dogara ga gumaka ba Yahweh ba.

zan tube ta tsirara, in nuna tsiraicinta kamar yadda yake a ranar da aka haife ta

Yahweh ba zai ci gaba da kare Isra'ila da kuma yi mata tanadi ba, domin kasar ta juya daga gare Shi. A Isra'ila, hakkin maza ne, bisa doka, su tanadi tufafi domin matayensu. Kin yin haka alama ce cewa namiji yana kin matarsa. Za a iya kara bayyana cikakkiyar ma'anar wannan.

zan maishe ta kamar hamada

Yahweh zai maida Isra'ila ta yi kama da hamada, wadda yanki ne busasshe mara amfani.

kuma zan sa ta mutu da kishirwa

A nan, "kishirwa" na nuni da bukatar sujada da dogaro ga Yahweh, ba gumaka ba, ko kuma Isra'ila ba za ta iya rayuwa a matsayin kasa ba.