ha_tn/heb/13/20.md

1.3 KiB

To

Wannan alama ce ta sabuwar sashe a wasiƙar. A nan, marubucin yana yaba wa Allah yana kuma yin addu'arsa na ƙarshe wa masu karatunsa.

wanda ya ta da babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu

"wanda ya tashi babban makiyayin tumakin, Ubangijinmu Yesu, zuwa ga rai"

daga matattu

Daga dukkan waɗanda sun mutu. Wannan furcin na bayani a kan dukkan mutanen da sun mutu da ke a ƙarƙashin ƙasa. Ta da mutum daga matattu na maganar sa mutumin yă sake zama da rai ne.

babban makiyayin tumakin

Ana maganar Almasihu a matsayinsa na shugaba da kuma mai tsaron dukkan waɗanda sun gaskata da shi ne kamar shi makiyayin tumaki ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta wurin jinin madawwamin alkawari

A nan "jini" na nufin mutuwar Yesu wadna shi ne tushen alkawarin da zai kasance har abada tsakanin Allah da dukkan masubi a cikin Almasihu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ya kammala ku da dukkan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa

"yă baku kowane abu nagari da kuke bukata domin ku iya aikata nufinsa" ko kuma "ya sa ku iya aikata kowane nagarin abu bisa ga nufinsa"

aiki a cikinmu

Kalmar nan "mu" na nufin marubucin da masu karatun. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

ga wanda ɗaukaka ta tabbata gare shi har abada

"wanda dukkan mutane za su yabeshi har abada"