ha_tn/heb/11/01.md

1.4 KiB

Mahaɗin Zance:

Marubucin ya faɗi abubuwa uku game da bangaskiya a wanna taƙaitaccen gabatarwa.

To

Ana amfani ne da wannan kalmar a nan domin a nuna canji daga ainihin koyarwa da ake yi. A nan marubucin ya fara bayyana ma'anan "bangaskiya".

Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu

AT: "Idan muna da bangaskiya, muna da tabbacin abubuwan da muke begensu" ko kuma "Bangaskiya ita cene abinda ke barin mutum ya sa zuciya da gabagaɗi a kan wasu abubuwa na musamman"

tabbaci

A nan wannan na nufin tabbacin alkawarai na Allah, musamman ma tabbacin cewa dukkan masubin Yesu za su kasance da Allah a sama har abada.

tabbatawar al'amuran da idanu basu gani

AT: "da har yanzu ba mu iya gani ba" ko kuma "da har yanzu ba su faru ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Domin ta wurin ta ne

"Domin suna da tabbaci game da abubuwan da basu faru ba tukuna"

kakanninmu suka sami yardar Allah

AT: "Allah ya yarda da kakanninmu domin suna da bangaskiya ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kakanninmu

Marubucin yana magana ne da Ibraniyawa akan kakanninsu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

aka hallicci duniya da umarnin Allah

AT: "Allah ya hallic duniya ta wurin ba ta umarni ta kasance" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba

AT: "Allah bai halita abubuwan da muke gani daga abubuwa da ake gani ba"