ha_tn/heb/10/19.md

2.8 KiB

'yan'uwa

Wato dukkan masubin Almasihu kenan, maza da mata. AT: "maza da mata" ko kuma "'yan'uwa masubi" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-gendernotations]])

wurin nan mafi tsarki

Wato gaban Allah kenan, ba wai wuri mafi tsarki da ke tsohon alfarwar ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta wurin jinin Yesu

A nan "jinin Yesu" na nufin mutuwar Yesu kenan. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

rayayyar hanya

Wannan na iya nufin 1) sabuwar hanyar zuwa wurin Allah da Yesu ya zama sanadiyar sa masubi su rayu har abada. ko kuma 2) Yesu yana da rai, kuma ta wurinsa ne masubi ke zuwa gaban Allah.

ta wurin labulen

Labulen da ke a haikalin duniya na wakilllcin maraban da ke tsakanin mutane da aihihin gaban Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta wurin jikinsa

A nan "jikinsa" na nufin jikin Yesu kenan, jikinsa kuma yana nufin mutuwarsa. AT: "ta wurin mutuwansa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

muna da babban firist a gidan Allah

Lallai ne a juya wannan a hanyar da zai bayyana a fili cewa Yesu ne wannan "babban firist."

a gidan

"mai mulki a gidan"

gidan Allah

Wannan na maganar jama'ar Allah kamar su ginannen gida ne. AT: "duk jama'ar Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

bari mu matso

A nan "matso" na nufin yi wa Allah sujada, kamar yadda firist zai haura zuwa haikalin Allah ya miƙa masa hadayar dabbobi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

da sahihiyar zuciya

"da amintattciyar zuciya" ko kuma "da zuciya mai gaskiya." A nan "zuciya" na nufin manufa mai kyau da ƙarfafawar masubi. AT: "da gaskiya" ko kuma "a gaskiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

cikakken gabagaɗi cikin bangaskiya

"da kuma gabagaɗin bangaskiya" ko kuma "da matuƙar dogara ga Yesu"

da zuciyarmu wadda aka tsarkake

AT: "kamar ya tsarkakke zuciyarmu da jininsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

zukatan da aka tsarkake

A nan "zuciya" na nufin lamiri, sanin abinda ke daidai da wanda ba daidai ba. Tsarkakewa na nufin samun gafara da kuma samun matsayin adalci. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

...

...

da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta

AT: "kamar ya wake jikunanmu da ruwa mai tsabta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta

Idan mau juyi ya fahimci wanna jumlar a matsayin baftismar Maibi, to ana nufin ainihin ruwa kenan, ba alama ba. Amma idan mai juyi na ɗauki ruwa a matsayin ainihin ruwa, to "tsabta" alama ce da ke nufin tsabta a ruhaniya da baftisma ke kawo wa. "Wankin" na nufin samun karɓa a gaban Allah na maibi. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])