ha_tn/heb/10/11.md

1.1 KiB

kulliyomi

"koda yaushe" ko kuma "kowace rana"

ba za su taɓa kawar da zunubai ba

Wannan na maganar "zunubai" ne kamar su wasu abubuwa ne da ake iya kawar da su. AT: "ba za su taɓa iya sa Allah ya gafarta zunubai ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ya zauna a hannun dama na Allah

A zauna "a hannun dama na Allah" misali ne na samun matuƙar daraja da iko daga Allah. Duba yadda aka juya wannan jumlar a [1:3]. AT: "ya zauna a wurin daraja da iko a gefen Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

har a maida maƙiyansa matashin sawayensa

Ana maganar yadda Almasihu zai ƙasƙantar da maƙiyansa ne kamar za a mayar da su wuri ne da zai ajiye kafafunsa a kai. AT: "har sai Allah ya ƙasƙantar da maƙiyansa su zama kamar kujera da zai sa kafafunsa a kai" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

waɗanda ake tsarkakewa

AT: "waɗanda Allah yake tsarkekewa" ko kuma "waɗanda Allah ya miƙa su ga kansa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)