ha_tn/heb/10/01.md

1.7 KiB

Mahaɗin Zance:

Marubucin yana nuna gazawar shari'a da hadayu, dalilin da ya sa Allah ya ba da shari'a, da kuma kammalawar sabuwar firistanci da kama hadayar Almasihu.

shari'a hoto ce kawai na kyawawan abubuwan da ke zuwa

Wannnan na maganar shari'a kamar ita wata hoto ce. Marubucin na nufin cewa ba shari'ar bane abu mai kyau da Allah ya alkawarta. Ya ɗan ambato kaɗan daga abubuwa masu kyaun da Allah zai yi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ba ainihin siffar waɗannan abubuwa ba

"ba ainihin abubuwan da kansu ba"

shekara da shekaru

"kowace shekara"

ba sai a daina miƙa hadayun ba?

Marubucin yana amfani ne da wannan tambaya ya sanar cewa ƙarfin hadayun sun gaza. "da sun daina yin hadayun" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

ɗaina yin

"tsayar da kasancewa"

da masu sujada sun samu tsarkakewa

A nan samun tsarkakewa nan nufin ba su kuma da wani hakin zunubi. AT: "da hadayun sun kau da zunuban su" ko kuma "Da Allah ya kawar masu da hakin zunubi" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

ba su san menene zunubi ba

"ba su san cewa suna da hakin zunubi ba" ko kuma "za su san cewa basu da wata hakin zunubi kuma"

Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awaii su kawar da zunubai

Ana maganar zunubai ne kamar wasu abubuwa ne da jinin dabba ke iya kawar da su yayin da yake zubowa. AT "Gama ba shi yiwuwa jinin bijimai da awaki su sa Allah ya gafarta zunubai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

jinin bijimai da na awaki

A nan "jini" na nufin mutuwar waɗannan dabbobi a matsayin hadayu ga Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)