ha_tn/heb/08/01.md

1.1 KiB

Mahaɗin Zance:

Bayan da murubucin ya unan cewa firistancin Almasihu ya fi firistancin duniya, ya kuma nuna cewa firistancin duniya yana kamanta salon na sama ne. Almasihu yana da babbar hidima, babbar alkawali.

Yanzu

Wannan bai nuna cewa "a daidain wannan lokacin ba", amma anyi amfani ne da shi domin a jawo hankalinmu zuwa wani bayani da ke biye.

muke ƙoƙarin cewa

Ko da shike marubucin yana amfani da wakilin suna da ke nuna mutum fiye da ɗaya, "mu," ba shakka yana magana game da shi kansa ne kawai. AT: "Ina cewa" ko kuma "Ina rubutawa"

ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba

Zai zauna a "hannun dama na Allah" alama ce na nuna samun wata babbar girma da iko daga Allah. Duba yadda aka fassara wannan a [1:3]. AT: "ke zaune a wurin girma da iko a gefen kurusiyi mai martaba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba

Mutane sukan gina haikali daga patan dabbobi, sai su manna shi a jikin wani katako, sai su shirya shi kamar wani bukka. A nan "haikali na gaskiya" na nufin haikali na sama da Allah ya ƙirƙiro"