ha_tn/heb/02/07.md

1.2 KiB

gaza mala'iku

Marubucin yana maganar yadda mutane sun gaza a muhimmanci kamar suna tsaye ne a matsayi da ya gaza matsayin mala'iku. AT: "basu da muhimmanci kamar mala'iku"

sa mutum ... Kã naɗa shi ... sawayensa ... gă shi

Waɗannan duka na nufin mutane gabaɗaya, a haɗe da maza da mata. AT: "sa mutane ... ka naɗa su ... sawayensu ... gă su" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-genericnoun]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-gendernotations]])

Ka naɗa shi da ɗaukaka da girma

Ana maganar kyautar ɗaukaka da girma kamar wata rawani ce a kan ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle. AT: "kã basu babban girma da ɗaukaka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ka kuma mallakar da komai a ƙarƙashin sawayensa

Marubucin yana maganar mulkin mutane bisa kowane abu kamar sun taka kowane abu da ƙafafunsu ne. AT: "ka basu mulki bisa kowane abu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Bai bar komai a keɓe ba

Wannan na nufin cewa dukkan abubuwa za su zama a ƙarƙashin Almasihu. AT: "Allah ya sa su suna mulki bisa dukkan komai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublenegatives)

har a yanzu ba mu ga yana sarayar da dukkan abubuwa ba tukuna

"Mun san cewa har yanzu mutane basu mulkin dukkan komai"