ha_tn/heb/02/05.md

1.3 KiB

Mahaɗin Zance:

Ambacin da ke nan daga littafin Zabura ne a Tsohon Alkawali. Ya cigaba har zuwa sashi na gaba.

Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa

"Allah bai sa mala'iku su yi mulki bisa"

duniyar nan da za a yi

A nan "duniya" na nufin mutanen da suke kasancewa a wurin. "za a yi" kuma na nufin duniya da za a yi bayan da Yesu ya dawo. AT: "mutanen da za su kasance a sabuwar duniya da za ayi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi?

Wannan tambayan ne da ke nanata cewa mutum ba komai ba ne, yana kuma nuna yadda ya zama abun mamaki yadda Allah ke sa hankalinsa a kansu. AT: "mutane ba komai bane, kuma duk da haka kana tunawa da su!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ko ɗan mutum ma, har da za ka kula da shi?

Wannan karin maganar "ɗan mutum" na nufin 'yan adam. Wannan tambayar na da ma'ana ɗaya ne da na farkon. Yana nuna yadda ya zama abun mamaki yadda Allah ke kula da mutane, wadda ba komai ba ne. AT: "Muhimmancin mutane kaɗan ne, duk da haka kana kula da su!" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] and rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ko ɗan mutum

AT: "ko wanene ɗan mutum" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)