ha_tn/heb/02/02.md

1.6 KiB

Idan kuwa maganar nan da aka faɗa ta bakin mala'iku

Yahudawa sun gaskanta da cewa Allah ya ba da shari'ar sa wa Musa ta wurin mala'iku. AT: "Idan kuwa maganar nan da Allah ya yi ta wurin mala'iku" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Idan kuwa maganar nan

Marubucin na da tabbaci cewa waɗannan abubuwa gaskiya ne. AT: "Domin maganar"

kowanne keta da rashin biyayya, sukan gamu da sakamako

A nan "keta" da "rashin biyayya" na tsaye ne a madadin mutanen da ke da laifin waɗannan zunuban. AT: "duk mutumin da ya yi zunubi ya kuma yi rashin biyayya zai gamu da sakamako" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

keta da rashin biyayya

Waɗannan kalmomi biyun a takaice na nufin abu ɗaya. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

ta ƙaƙa za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka?

Marubucin na amfani ne da wannan tambaya domin ya nanata cewa mutanen za su gamu da hukunci idan sun ƙi ceton Allah ta wurin Almasihu. AT: "lallai ne Allah zai hukunta mu idan ba mu kasa kunne ga maganarsa game da yadda zai cece mu ba!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ƙi

"ƙi kasa kunne" ko kuma "ɗauke shi da rashin muhimmanci"

Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da wannan sakon ceton, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi

AT: "Ubangiji ne da kansa ya fara sanar da wannan sako game da yadda Allah zai cece mu, sa'annan waɗanda suka ji sun tabbatar mana da shi" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-abstractnouns]])

yadda ya nufa

"yadda dai yake so ya yi"