ha_tn/heb/01/13.md

1.3 KiB

Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taɓa ... ƙafafu"?

Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan don ya nanata cewa Allah bai taɓa faɗin haka wa wani mala'ika ba. AT: "Amma Allah bai faɗa wa wani mala'ika ... ƙafafu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Zauna a hannun dama na

A zauna a "hannun dama na Allah" wata alama ce ta samun babban girma da iko daga Allah. AT: "Zauna a wurin girma a gefe na" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

sai na sa makiyanka a ƙařƙashin ƙafafunka

Ana maganar maƙiyan Almasihu kamar za su zama wani abun taka wa ne da sarki ke taka wa da ƙafafunsa a fãda. Wannan sifar na nuna nasara da rashin daraja ga maƙiyansa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi ... gãji ceto ... ?

Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan domin ya tunashe da masu karanta wannan wasiƙar cewa mala'iku basu da iko kamar Almasihu, amma suna da nasu hidima dabam. AT: "Dukkan mala'iku ruhohi ne waɗanda ... gaji ceto" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

wa waɗanda za su gãji ceto

Ana maganar samun abinda Allah ya alkawarta wa masubi kamar gadan dukiya ne ko kuma arziki daga wani ɗan iyali. AT: "ga dukkan waɗanda Allah zai ceta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)