ha_tn/heb/01/06.md

908 B

Ɗan fãri

Wato Yesu kenan. Marubucin yana ce da shi "ɗan fãri" ne domin ya nanata muhimmanci da ikon Ɗan a bisa kowa. Wannan bai nuna cewa Yesu ya taɓa fara kasancewa a wani lokaci a baya ba ko kuma cewa Allah yana da wasu 'ya'ya kuma kamar Yesu ba. AT: "Ɗansa mai girma, tilonsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ya ce,

"Allah ya ce"

Shi ke mayar da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta

Wannan na iya nufin 1) "Allah ya sa mala'ikunsa su zama ruhohi, masu bauta masa da iko kamar harsunan wuta" ko kuma 2) Allah ya sa iska da harsunan wuta su zama ''yan aika da kuma masu hidimarsa. A ainihin harshen, kalmar nan "mala'ika" na da ma'ana ɗaya da "ɗan aika" sa'annan kalmar nan "ruhohi" na da ma'ana ɗaya da "iska." Ko ma ta yaya, kwayar maganar itace mala'ikun suna bauta wa Ɗan domin ya fi su girma. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)