ha_tn/heb/01/01.md

2.2 KiB

Muhimmin Bayani:

Kodashike wannan wasiƙar bata ambaci masu karɓan ta ba waɗanda aka aika masu, marubucin dai ya rubuto wannan wasiƙar musamman zuwa ga Yahudawa, waɗanda sun fi fahimtar misalai da dama da ya bayar daga Tsohon Alkawari.

a zamanin nan na ƙarshe

"a waɗannan kwanakin ƙarshen." Jmlar na nufin lokacin da Yesu ya fara hidimarsa, har zuwa sa'ada Allah zai ƙaddamad da cikakken mulkin sa a bisa halitarsa.

ta wurin Ɗan

"Ɗa" a nan wata laƙabi ce mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

ya zama magajin komai

Marubucin yana maganar Ɗan kamar zai gaji wata arziki ne ko dukiya daga Ubansa. AT: "yă mallaki dukan komai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ta wurin sa ne Allah ya halici duniya

"Ta wurin Ɗan ne Allah ya halici dukkan komai"

hasken ɗaukakar Allah

"hasken ɗaukakarsa." A nan an haɗa ɗaukakar Allah ne da wuta mai haske kwarai. Marubucin yana cewa Ɗan yana ɗauke da hasken, yana kuma wakilcin ɗaukakar Allah.

ɗaukaka, ainihin kamaninsa

"ɗaukaka, sifar Allah." "Ainihin kamaninsa" ya na da ma'ana kusan ɗaya ne da "hasken ɗaukakarsa." Ɗan yana ɗauke da hali da allahntakar Allah, yana kuma wakilcin dukkan koman da Allah yake. AT: "ɗaukaka yana kuma kamar Allah" ko kuma "ɗaukaka, kuma abinda ke gaskiya game da Allah, gaskiya ne game da Ɗan"

kalmar ikonsa

"kalmarsa mai iko." A nan "kalma" na nufin wata sako ko umurni. AT: "umurnin sa mai iko" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Bayan da ya tsarkake zunubanmu

"tsarkakewa" AT: "bayan da ya gama tsarkakemu daga zunubanmu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

da ya tsarkake zunubanmu

Marubucin yana maganar gafarar zunubai kamar tsarkake mutum ne. AT: "ya sa shi abu mai yiwuwa Allah yă gafarta zunubanmu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

sai ya zauna a hannun dama na maɗaukaki

Zama a "hannun damar Allah" alama ce na samun girma da iko daga wurin Allah. AT: "yana zaune a wurin girma da iko a gefen Zatinsa a can sama" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

Zatinsa a can sama

A nan "Zatinsa" na nufin Allah. AT: "Allah maɗaukaki" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)