ha_tn/gen/44/16.md

1.3 KiB

Me za mu cewa shugabana? Me za mu faɗa? Ko yaya zamu baratar da kanmu?

Duk tambayoyin guda uku suna nufin dai-dai ne abu ɗaya. Suna amfani da waɗannan tambayoyin don jaddada cewa babu wani abin da za su iya faɗi don bayyana abin da ya faru. AT: "Ba mu da abin da za mu ce, ya shugabana. Ba za mu iya faɗi komai mai mahimmanci ba. Ba za mu iya baratar da kanmu ba." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Allah ya gãno laifin bayinka

Anan "gano" ba yana nufin Allah ne kawai ya gano abin da 'yan'uwa suka aikata ba. Wannan yana nufin Allah yana azabta su saboda abin da suka aikata. AT: "Allah yana yi mana horo game da zunubanmu na baya"

dukkan mu da wanda aka iske kofin a hannunsa

Anan "hannun" yana tsaye ga mutum gaba ɗaya. Hakanan, "an samo" za'a iya bayyana shi a cikin tsari mai aiki. AT: "wanda ya sami ƙoƙon ku" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Mutumin da aka iske kofin a hannunsa, wannan taliki zai zama bawana

Anan "hannun" yana tsaye ga mutum gaba ɗaya. Hakanan, "an samo" za'a iya bayyana shi a cikin tsari mai aiki. AT: "Mutumin da yake da ƙoƙo na" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])