ha_tn/gen/33/09.md

1.6 KiB

Ina da isassu

Kalmar "dabbobi" ko "kaya" an fahimce ta. AT: "I na da isassun dabbobi" (UDB) ko "I na da isassun kaya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

idan na sami tagomashi a idanunka

A nan "idanunka" na nufin tunani ko ra'ayin mutum. AT: " idan na sami tagomashi a idanunka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

kyauta ta daga hannuna

A nan "hannu" na nufin Yakubu. AT: "wadan nan kyaututtuka da na ke baka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

hannu na, domin da gaske

Za'a iya fasara wannan a matsayin sabuwar jimla. "hannu na. Domin tabbas"

na ga fuskar ka, kuma kamar ganin fuskar Allah ne

Ma'anar wannan batu nada dan duhu. Mai yiwuwa ma'anar ta zama 1) Yakubu na murna cewa Isuwa ya gafarta masa kamar yadda Allah ya gafarta masa ko 2) Yakubu na mamakin sake ganin dan'uwansa kamar yadda yayi mamakin ganin Allah ko 3) Yakubu ya natsu domin zuwa gaban Isuwa kamar yadda ya natsu a gaban Allah. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

na ga fuskar ka

A nan "fuska" na nufin Isuwa. Yana da kyau a fasara "fuska" saboda amfanin kalmar a nan da "fuskar Allah" da "fuska da fuska" a Farawa 32:29. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

da aka kawo maka

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "wanda bayina suka kawo maku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Allah ya aiwatar da alheri zuwa gare ni

"Allah yayi mani da kyau" ko "Allah ya albarkace ni sosai"

Yakubu ya lallashe shi, Isuwa kuma ya karɓe su

Abin da aka saba ne aƙi amsar kyauta da farko, amma sai a amsa kafin mai badawa ya yi fushi.