ha_tn/gen/25/23.md

997 B

yace da ita

"yace da Rebeka"

Al'umma biyu ... bauta wa ƙaramin

Wannan yaren waƙa ne. Idan harshen ka na da tanadi domin waƙa, zaka iya yin amfani da wannan a nan. (Duba: rc://*/ta/man/translate/writing-poetry)

Al'umma biyu ce a mahaifarki

A nan "al'umma biyu" na nufin yara biyun. Kowannan yaro zai zama uba ga al'umma. AT: "al'umma biyu zata fito daga yan biyun da ke tare da ke" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

mutane biyu kuma zasu rabu daga gare ki

A nan "mutane biyu" na matsayin yara biyun. Kowanne zai zama uba ga al'umma. Za'a iya fasara wannan da aikatau. AT: "yayin da kika haifi wadannan yaran zasu yi gaba da juna" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

babban kuma zai bauta wa ƙaramin

Ma'anar Wannan sune 1) "babban yaro zai bautawa ƙaramin yaro" ko 2) "zuriyar babban zata bautawa zuriyar ƙaramin." Idan zai yiwu, a fassara shi yadda mutane zasu fahimci kowacce ma'ana.