ha_tn/gen/24/12.md

2.0 KiB

Sai ya ce

"Sai bawan ya ce "

ka ba ni nasara a yau ka kuma nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim

Za ka iya furta wanna da kalmar "ta wurin." Wannan ya nuna a zahiri yadda bawan ya ke son Allah ya cika alkawarin sa. AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim ta wurin bani nasara yau" (Duba: rc://*/ta/man/translate/writing-connectingwords)

ka ba ni nasara

"ka ba ni nasara." Bawan na so ya samarwa yaron Ibrahim mata nagari. Kalmar "nasara" zata iya zama aikatau. AT: "ka taimake ni don inyi nasara" ko "ka bani ikon yin abin da ya kawo ni nan" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim

Wannan aminci ne saboda alkawarin da Allah ya yi da Ibrahim. Kalmar "amintaccen" za'a iya cewa "ka yi aminci." AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

Duba

A nan kalmar "duba" ta ƙara armashi ga abin da ya biyo.

ƙoramar ruwa

"ƙoramar ruwa" ko "rijiya"

'yan'matan mutanen birnin

"'yan'matan birnin"

Ka sa abin ya kasance kamar haka

"Ka sa abin ya kasance kamar haka" ko "bari haka ya kasance"

In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha

Wannan magana ce a bakã cikin wata bakã. Za'a iya bayyana hakan a fakaice. AT: "In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-quotesinquotes]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-quotations]])

ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki

Matan suna ɗaukar abin ɗibar ruwa a kafaɗa. Sai ta saukar kafin ta ba namiji ruwa in ya bukata.

abin ɗibar ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa

ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana

Kalmar "amintacce" za a iya cewa "zama da aminci". AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)