ha_tn/gen/22/15.md

1.4 KiB

na biyu

Kalmar "na biyu" ita ce ƙa'ida ta biyu. AT: "sake" (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-ordinal)

kuma yace - wannan shi ne furcin Yahweh

"faɗa saƙon nan daga Yahweh" ko "furta waɗannan kalmomin daga Yahweh." Wannan na nufin cewa maganar ta zo daga Yahweh ne kai tsaye.

na yi rantsuwa da kaina

"Na yi alkawari kuma ni ne shaida." Kalmar "rantsuwa da" na da ma'anar wani abu ko wani mutum da shine tushi ko na da iko bisa alkawarin da aka yi. Ba wani abu da ke da iko fiye da Yahweh da zai yi rantsuwa da shi.

ka yi wannan abu

"ka yi mini biyyaya"

zan kuma ruɓanɓanya zuriyarka

"Zan sa zuriyarka su yi ta karuwa" ko "Zan sa zuriyar ka su yi yawa"

kamar taurarin sammai, kamar kuma yashin da ke gaɓar teku

Allah na kamanta yawan zuriyar Ibrahim da taurari da yashi. Kamar yadda mutane ba za su iya kirga taurari ko yashi ba, haka zuriryar Ibrahim za su yawa da mutane ba za su iya kirga wa ba. AT: "fiye da abun da za ka iya kirgawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kamar taurarin sammai

"sammai" a nan na nufin dukka abun da ke sama da duniya, da rana, wata, da kuma taurari.

za su mallaki ƙofar maƙiyansu

Anan "ƙofar" na wakiltar birnin gaba ɗaya. "mallaki ƙofar maƙiyansu" na ma'anar hallakar da aƙiyansu. AT: "samu cikaken nasara bisa maƙiyansu" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]])