ha_tn/gen/20/08.md

1007 B

Ya faɗa musu duk waɗanna abubuwa

"Ya faɗa musu dukka abubuwan da Allah yace da shi"

Me kenan ka yi mana?

Abimelek na amfani da tambaya ya tuhume Ibrahim. AT: "Ka aikata mana mumunar abu!" ko "Duba abin da ka yi mana!" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Yaya na yi maka laifi, da ka jawo ... zunubi?

Abimelek na amfani da tambaya ya tunashe Ibrahim cewa bai yi masa zunubi ba. AT: "Ban yi maka laifin komai ba da har za ka kawo ... zunubi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

a ka jawo wa mulkina da ni kaina wannan babban zunubi

Ana maganar sa mutum ya aikata laifi kamar wani abu ne da ake iya ɗaura wa wani a kai. AT: "da zaka ɗaura wa ni da mulkina aikata irin wannan mumunar zunubi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

a bisa mulkina

"mulki" a nan na nufi mutane ne. AT: "a bisa mutanen da nake mulki" ( Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba

"Bai kamata ka yi mini haka ba"